Obasanjo na yi wa Buhari zagon-kasa - 'Yan majalisa

Obasanjo na yi wa Buhari zagon-kasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Olusegun Obasanjo ya sha jawo ce-ce-ku-ce a Nigeria

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun ce tsohon Shugaban kasar Olusegun Obasanjo na yi wa gwamnatin Buhari zagon-kasa, bayan da ya zarge su cin hanci da rashawa.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta bayyana Obasanjo a matsayin "mutumin da ya fi kowa cin hanci a tarihin kasar".

Mai magana da yawun majalisar Hon Abdulrazak Namdas ya ce "Abin takaici ne ya fara nuna halayyarsa ta kawar da gwamnati da aka sanshi da ita tun shekara 1979".

Ya kara da cewa "Ya yi hakan ga tsofaffin Shagabanni da suka hada da Shehu Shagari, Janar Buhari, Janar Babangida, da kuma Janar Abacha kafin ya daure shi a kurkuku".

Olusegun Obasanjo, ya furta wadansu kalamai a ranar Laraba a Lagos, inda ya soki gwamnatin Buhari saboda yadda take yi wa gwamnatoci ukun da suka gabata, ciki har da ta sa, kudin goro wajen zargin rashin iya jagoranci.

Ya kuma bai wa Buhari shawara da ya daina korafi kan abin da ya wuce, inda ya ce tun da an zabe shi ne domin ya gyara Nigeria, ya kamata ya mayar da hankali kan gyara barnar da ya tarar.

Sannan ya nemi ya taka wa 'yan majalisun kasar birki, yana mai cewa majalisar ce dandalin cin hanci da satar kudin al'umma.

Sai dai Namdas ya ce a lokacin Obasanjo ne aka baje kudi a majalissar tarayya domin bayar da cin hanci, saboda a sauke Kakakin Majalisar na wancan lokaci Ghali Umar Na Abba.

Ya kuma tambayi 'yan Nigeria cewar "Shin har kun manta lokacin da Obasanjo ya yi amfani da karfin ikonsa, inda ya dunga karbar kudade daga wajen 'yan kasuwa da 'yan kwangila domin gina katafaren dakin karatunsa?

Ya kuma ce Obasanjo ya taimakawa Buhari a lokacin yakin zabe, amma tun lokacin da ya fahimci cewar gwamnati mai ci tana fama da tattalin arziki, sai ya juya da nufin yi mata zagon kasa.

Kawo yanzu Mista Obasanjo bai ce komai game da kalaman na 'yan majalisar ba.