An tsare mai shirya fina-finai saboda zargin sace wayoyin hannu

Kotun Nigeria

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

An tsare mai shirya fim kan zargin sace wayoyi

Wata kotu a jihar Legas ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare fitatcen mai shirya fina-finai Yarabanci, Seun Egbede, bayan da aka zarge shi da satar wayoyin hannu kirar iPhone guda goma.

Sai dai kuma Egbegbe - wanda ya yi hadakar aiki tare da jarumar fim Toyin Aimakhu - ya karyata zargin.

Masu shigar da kara sun zarge shi da arcewa da gudu daga kantin da ya kwashe wayoyin ya kuma fada cikin wata mota da ke a jiransa, a lokacin da mai wurin yake lissafa kudin wayoyin.

An dai kama shi daga baya, inda aka lakada masa duka, kafin jami'an tsaro suyi awon gaba da shi, in ji jaridar Vanguard.

An samu hatsaniya a cikin kotun da ke Ikeja, bayan da magoya bayan mai shirya fim din suka yi barazanar daukar mataki kan duk wanda ya dauki hotonsa.