An gano kawuna da gangunan jikin mutane a manyan kaburra a Mexico

An gano gawarwakin ne a manyan kaburra 17 a yankin da masu safarar miyagun kwayoyi ke cin karensu babu babbaka

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An gano gawarwakin ne a manyan kaburra 17 a yankin da masu safarar miyagun kwayoyi ke cin karensu babu babbaka

Hukumomi a kasar Mexico sun gano gawarwakin mutum 32 da kuma kawunan mutum tara da aka binne a wasu manyan kaburbura a yankin da masu safarar miyagun kwayoyi ke cin karensu babu babbaka.

Masu bincike sun hako gawarwakin na maza 31 da mace guda daya a yankin Zitlala, wanda ya yi karin-suna wajen samun rashin jituwa tsakanin kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi.

Kakak,in rundunar tsaron kasar ya bayyana gano gawarwakin da cewa "wani babban abin tayar da hankali ne", a yayin da ake ci gaba da neman wasu gawarwakin.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda aka kama game da wannan batu.

An binne mutanen ne a cikin kaburbura 17 a kusa da kauyen Pochahuixco tsakanin ranar Talata da Alhamis.

Kakakin rundunar ta tsaro Roberto Alvarez ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa an gano kaburran ne bayan an tseguntawa jami'an tsaro labarin binne su.

AFP ya ruwaito cewa an gano kawunan mutum hudu "a cikin nau'rar da ke sanyaya ruwa."

Yankin dai, wanda ke jihar Guerrero, ya shahara wajen aikata miyagun laifuka da samar da hodas libilis.

Rahotanni na cewa an kashe mutum 1,800 tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban shekarar nan a yankin.