Babban kwamandan IS a Australia na nan da rai

Ana zargin Prakash, wanda aka fi sani da Abu Khaled al-Cambodi, da hannu a kai hare-haren da aka kitsa a Australia

Asalin hoton, Al Hayat Media Center

Bayanan hoto,

Ana zargin Prakash, wanda aka fi sani da Abu Khaled al-Cambodi, da hannu a kai hare-haren da aka kitsa a Australia

Dan kasar Australian nan da ke yi wa kungiyar IS yaki, wanda aka yi zaton an kashe, yana nan da ransa amma a daure a yankin gabas ta tsakiya, in ji wasu rahotanni.

A watan Mayu ne gwamnatin Australia ta ce an kashe Neil Prakash, babban mayakin IS, a wani hari da jirgin Amurka ya kai masa.

Antoni Janar na kasar George Brandis ya ce an kashe shi ne a birnin Mosul na Iraki.

Amma wasu rahotanni da jaridar New York Times ta wallafa ranar Juma'a sun ambato wasu majiyoyi na manyan jami'an tsaron Amurka na cewa Prakash yana nan da ransa.

Gidan rediyon Australia ya ce Prakash ya mika kansa ga hukumomin Turkiyya makonni da dama da suka wuce.

Mataimakin ministan ma'aikatar yaki da 'yan ta'adda Michael Keenan, ya ce gwamnati ba za ta ce komai a kan wannan sabon labari ba.

Ana zargin Prakash, wanda aka fi sani da Abu Khaled al-Cambodi, da hannu a kai hare-haren da aka kitsa a Australia kuma ya fito a bidiyo da mujallu inda yake watsa manufofin IS.