Kasashen Turai za su bai wa Birtaniya mamaki

Joseph Muscat
Bayanan hoto,

Joseph Muscat ya ce ba za su rangwanta wa Birtaniya ba

Firai ministan Malta ya ce ba wasa suke yi ba da suka ce ba za su bari Birtaniya ta rika kasuwanci da su ba tare da ta biya haraji ba kuma ta hana 'yan kasashensu shiga cikin ta ba tare da shamaki ba bayan ta fice daga Tarayyar Turai.

Joseph Muscat, wanda kasarsa za ta karbi shugabancin kungiyar Tarayyar Turai a watan Janairu, ya shaida wa BBC cewa "wannan shi ne hakikanin matsayinmu kuma ba za mu sauya ba".

Firai ministar Birtaniya Theresa May ta ce kasarta za ta soma shirye-shiryen ficewa daga Tarayyar Turan a watan Maris.

Amma Mr Muscat ya ce za a iya jinkirta tattaunawa kan sabuwar dangantakar da za ta kasance tsakanin Birtaniya da kasashen Tarayyar Turan.

Yawancin hasashen da aka rika yi ya ta'allaka ne kan yadda Birtaniya za ta fice daga Turai salin-alin ta yadda za a bar ta ta rika kasuwanci da sauran kasashe ba tare da ta biya haraji ba, yayin da ita kuma za ta yi sassauci kan dokokin shige-da-ficenta.

Sai dai Mr Muscat ya ce dole ne Birtaniya da kasashen Tarayyar Turan su amince da sababbin sharuddan dangantaka a tsakaninsu kafin, a hukumance, Mrs May ta sanar da su kasarta za ta fice daga tarayyar.