Ibrahimovic ya ce babu dan wasa kamar Rooney

Asalin hoton, Reuters
Zlatan Ibrahimovic ne ya taimaka wa Rooney ya zura kwallon farko
Zlatan Ibrahimovic ya ce takwaran wasansa a Manchester United Wayne Rooney dan wasa ne da "babu kamar sa" kuma ya kamata a sake jinjina masa bayan kyaftin din na Ingila ya kafa tarihi na zama dan wasan kungiyar da ya fi kowanne zura kwallo a gasar Turai a wasan da suka doke Feyenoord 4-0.
Rooney, mai shekara 31, ya ci kwallonsa ta 39 a wasannin Turai bayan United ta yi nasara a wasan na ranar Alhamis, inda ya ba su damar shiga rukunin 'yan 32 na gasar Europa.
Hakan na faruwa ne a lokacin da Rooney, wanda saura maki daya ya yi kan-kan-kan da Sir Bobby Charlton wanda ya zura wa kungiyar kwallo 249, ya kare kansa bayan an wallafa wasu hotuna da ke nuna shi ya bugu da giya a lokacin da suka bar Ingila domin yin wasa.
Ibrahimovic ya shaida wa BBC cewa Rooney, "Dan wasa ne haziki da babu irin sa. Ina farin ciki da ya kafa wannan tarihi. Zan taimaka masa ya sake cin kwallo domin sake kafa wani tarihin wanda ya fi wannan muhimmanci."
Rooney ya nemi gafara a makon jiya bayan an wallafa hotunan nasa.
Sai dai a ranar Asabar din da ta gabata ya ce an nuna son kai kan rahotannin da aka watsa game da lamarin, yana mai cewa hakan ya nuna cewa "kafafen watsa labarai na son ganin bayana."