Kasashen duniya suna tsokaci kan mutuwar Castro

Putin ya ce ba za a manta da Castro ba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Putin ya ce ba za a manta da Castro ba

Shugabannin kasashen duniya sun soma mayar da martani bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro, wanda ya rasu yana da shekara 90.

A kasar India - wacce kawa ce ta kut-da-kut ga Cuba - Firai Minista Narendra Modi ya bayyana Fidel Castro a matsayin "daya daga cikin gwarzayen karni na 20."

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa India tana makokin babban abokinta.

A can Rasha ma, Shugaba Vladimir Putin ya mika ta'aziyyarsa ga Shugaba Raul Castro, yana mai cewa: "Za a rika tunawa da wannan mutumin kirkin a matsayin wata alama ta wani karni a tarihin duniya."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zuma ya ce Fidel Castro ya taimaka wajen fafutikar Afirka ta kudu

Shugaban kasar Mexico Enrique Peña Nieto shi ma ya bayyana dan gwagwarmayar da cewa yana daya daga cikin mutanen da suka fi shahara a karnin da ya wuce, yana mai cewa babban amini ne ga kasarsa.

A nasa bangaren, shugaban kasar Afirka ta kudu, Jacob Zuma ya nuna alhinin rasuwar Castro, yana mai cewa ya bai wa 'yan Afirka gagarumin goyon baya a lokacin da suke fafutikar ganin bayan mulkin farar-fata na zalunci.