Hatsarin jirgin kasa a Iran ya kashe mutum 31

Jirgin da yayi hatsari a Iran

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An samu cikas a aikin ceto kasancewar hatsarin ya auku ne a wajen gari

Akalla mutum 31 ne suka rasa rayukansu kuma mutane da dama sun jikkata a wani hadarin jirgin kasa a arewacin Iran.

A safiyar ranar Juma'a ne taragwan jirgin suka kauce daga kan layin dogo kuma daga bisani suka kama da wuta bayan da ya lalace a tsakanin tashoshin jiragen kasa kuma wani jirgin ya doke shi.

Hatsarin ya auku ne a wurin da ke da nisan kilomita 250 daga gabashin Tehran, babban birnin kasar.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa hudu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu ma'aikatan tashar jirgin kasa ne.

Gwamnar jihar, Mohammad Reza Khabbaz ya shaida wa manema labarai na kasa cewa an gano gawarwaki 31 kuma ana bai wa sama da mutane 70 kulawa a asibiti.

Hadarin dai ya auku ne a lardin Semnan da ke arewacin kasar Iran a tsakanin Tehran da Mashhad a arewa masogabas.

Hassan Shokrollahi, daraktan kungiyar agaji ta Red Crescent, ya ce an samu cikas a aikin ceto kasancewar hadarin ya auku ne a wajen gari.