An nemi a sake ƙirga ƙuri'un zaben shugaban kasa a Amurka

Kawo yanzu dai Donald Trump bai ce komai ba game da batun

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Kawo yanzu dai Donald Trump bai ce komai ba game da batun

Jam'iyyar Green Party a Amurka ta nemi a hukumance da a sake ƙidaya ƙuri'un da aka kada na zaben shugaban kasar a jihar Wisconsin, inda Donald Trump ya samu nasara lashewa da 'yar ƙaramar tazara.

Jami'ai a jihar sun ce tuni suka fara shirye shiryen sake ƙirga ƙuri'un sakamakon bukatar hakan da aka gabatar.

Jam'iyyar dai tana fatan cewa matakin data dauka zai iya zaburar da bukatar neman sake ƙirga ƙuri'un a jihohin Pennsylvania da Michigan.

Wasu kafafen watsa labarai a Amurka sun ce 'yar takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Green din Jill Stein na son tabbatar da cewa masu kutse a kwamfuta basu karkata yadda sakamakon zaben ya kasance ba ga Mr Trump.

Wasu masana dai na ganin wajibi ne sai idan sakamakon jihohin uku sun sauya gaba daya kafin su iya canza makomar zaben kasar lamarin da masanan ke ganin abu ne da kamar wuya.

A bangare guda kuma tuni zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sake yin nadin wasu jami'ai biyu yayin da yake ci gaba da nadin mukarraban da za su yi aiki a gwamnatin sa.

An nada Kathleen Macfarland mai sharhi a kafar watsa labaran Fox News matsayin mataimakiyar mai ba shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro yayin da ya nada Don McGahn,wani lauya a kwamitin yakin zaben sa a matsayin mashawarci akan fadar White House.

Wasu rahotanni sun ce ana ta tada jijiyoyin wuya tsakanin wasu manyan masu ba Mr Trump shawara kan mutumin daya kamata ya nada a matsayin mukamin sakataren harkokin wajen kasar dake da matukar muhimmanci.

Kakakin Mr Trump din Kellyanne Conway, ta bayyana adawarta game da shawarar nadin Mitt Romney wanda ya yi kaurin suna wajen sukar Mr Trump tsakanin 'yan jami'iyyar Republican a matsayin sakataren harkokin wajen kasar.