Tsohon shugaban ya rasu ya na da shekara 90

Fidel Castro
Bayanan hoto,

Fidel Castro ya rasu ya na da shekara 90

Gidan talabijin din kasar Cuba, ya sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar Fidel Castro.

Ya rasu ya na da shekaru 90 a duniya.

Dan uwan marigayin Raul Castro shi ne ya sanar da rasuwarsa, wanda tun a shekarar 2006 ya maye gurbinsa.

Da misalin karfe goma da rabi na dare ne tsohon shugaban kuma kwamandan juyin juya halin ya rasu.

Fidel Castro ya dare karagar mulki ne bayan hambarar da gwamnatin shugaba Fulgencio Batista a shekarar 1959.