FA ba za ta hukunta Rooney kan buguwa da giya ba

Wayne Rooney

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wayne Rooney ya ce 'yan jarida na son ganin bayansa

Hukumar kwallon kafar Ingila ba za ta hukunta kyaftin din kasar Wayne Rooney ba bayan da aka wallafa wasu hotunasa ya bugu da giya lokacin da suka tafi kasashen waje domin yin wasa.

Dan wasan na Manchester United ya nemi gafara saboda daukar hotunan "da ba su dace ba" kwana daya bayan wasan cancantar neman shiga gasar cin kofin duniya da suka doke Scotland.

Wasu jiga-jigan hukumar FA sun tabbatar wa Rooney, mai shekara 31, cewa ba za a hukunta shi ba.

Jaridar Daily Mirror ta bayar da rahoton da ke cewa FA ta gano an gayyaci Rooney wajen bikin aure ne lokacin da ya sha giyar kuma ba a kafa dokar hana fita a ranar ba.

An yi binciken ne bayan jaridar The Sun ta wallafa hotunan na Rooney a wajen shagalin da tsakar daren ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamba.

Kazalika FA na yin bincike kan rahotannin da ke cewa 'yan wasa da dama sun raba-dare bayan wasan da suka ci Scotland 3-0.

Rooney dai ya zargi 'yan jarida da zuzuta labarain, yana mai cewa so suke yi su ga bayansa.