'Yan kasar Cuba na ci gaba da jimamin mutuwar Fidel Castro

Candles and flowers around a picture of Fidel Castro in Havana. Photo: 26 November 2016

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Za a kwashe kwana tara ana makoki

'Yan kasar Cuba na alhinin mutuwar tsohon shugabansu dan gwagwarmaya Fidel Castro, wanda aka bayar da sanawar mutuwarsa ranar Juma'a.

An sassauto da tutocin kasar a lokacin da 'yan kasar suka fara makokin kwana tara kan mutuwar tasa.

Daga ranar Litinin, za a bar mutane su je gaban gawarsa domin nuna girmamawa kafin a kone ta sannan ta dauki tokar zuwa Santiago de Cuba inda ya fara fafutikar kwatar mulki.

Shugabannin kasashen duniya da dama sun mika ta'aziyyarsu ga gwamnatin kasar.

Sai dai zababben shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Castro a matsayin "mai mulkin kama-karya."

Castro ya soma mulki ne a shekarar 1959 bayan ya jagoranci juyin-juya-hali na Kwanimisanci, kana ya shafe shekara da shekaru yana bijirewa Amurka.

Masu goyon bayansa suna yi masa kallo a matsayin wanda ya kalubalanci Amurka a lokacin yakin cacar-baki sannan ya mayar wa da Cuba martabarta.

Sai dai masu sukarsa suna bayyana shi a matsayin mai mulkin kama-karya.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Castroa tsakiyar shekarar 1950 tare da wani dan gwagwarmayar - Che Guevara

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Castro ya gana da Paparoma John Paul II, duk da cewa ya ayyana kasar Cuba a matsayin wacce ke bin addinin gargajiya

  • 1926: An haife shi a Oriente, lardin da ke yamma maso gabashin Cuba
  • 1953: An daure shi bayan ya jagoranci wani yunkurin tumubuke gwamnatin Batista da bai yi nasara ba
  • 1955: An sake shi daga gidan yari bayan an yi masa afuwa
  • 1956: Shi da Che Guevara suka fara yakin sari-ka-noke
  • 1959: Ya kayar da Batista, inda ya zama Firai Ministan Cuba
  • 1961: Ya yaki mamayar da kungiyar Bay of Pigs, wacce CIA ke mara wa baya
  • 1962: Ya tayar da jijiyoyin wuya kan makamai masu linzami bayan ya amince cewa tsohuwar tarayyar Sobiat za ta iya aikewa da makaman zuwa Cuba
  • 1976: Majalisar dokokin Cuba ta zabe shi a matsayin shugaban kasa
  • 1992: Ya cimma jarjejeniya da Amurka kan 'yan gudun hijirar Cuba
  • 2006: Ya sauka daga shugabancin kasar saboda rashin koshin lafiya