Dakarun Syria sun ƙwace wani yanki na Aleppo

Dakarun gwamnatin Syria sun ci gaba da luguden wuta a wasu yankuna na Aleppo dake hannun 'yan tawaye

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Dakarun gwamnatin Syria sun ci gaba da luguden wuta a wasu yankuna na Aleppo dake hannun 'yan tawaye

Kafafen yada labarai na gwamnatin Syria sun ce dakarun kasar sun sake karbe iko na wani yanki mai girma dake gabashin birnin Aleppo daga hannun 'yan tawaye.

Kafafen yada labaran sun ruwaito cewa a halin yanzu dakarun gwamnati na karaɗe yankin Masaken Hanano don kwance nakiyoyi da 'yan tawayen suka binne a kasa.

Fiye da mutane dubu dari uku ne aka yiwa kawanya a gabashin Aleppo, yankin da aka yi ta luguden wuta tun bayan da dakarun gwamnati suka ci gaba da kai farmaki a farkon wannan watan.

A bangare guda kuma dakarun Amurka da ke jagorantar ƙawancen sun tabbatar da rasuwar daya daga cikin manyan sojojin da ke jan ragamar aikin a bata kashin da suka yi da mayakan masu ikirarin jihadi na kungiyar IS.