Malaysia: Za'a hukunta wani mai zanen barkwanci

Asalin hoton, Getty Images
Ana ta kiraye kiraye ga Firai minista Najib Razak da ya yi murabus saboda zargin sa a badakalar wasu kudade
An tsare wani fitaccen mai zanen barkwanci a kasar Malaysia bayan da ya yi zanen da ake zargin ya ci mutuncin Firai ministan kasar Najib Razak.
'Yan sanda sun tsare Zulkiflee Anwar Ulhaque wanda aka fi sani da suna Zunar ne bisa zargin sa da saba dokar data hana harzuka mutane su yi wa hukumomi bore.
Yana kuma fuskantar wasu tuhume tuhume har guda tara.
Zane zanen barkwanci da Zunar kan yi dai su kan yi nuni ne da zargin da ake yi cewa Firai ministan kasar nada hannu dumu-dumu a fadakalar biliyoyin daloli na wasu kudaden gwamnati da aka ware a wata gidauniya ta musamman.
A kwanakin baya ne Jami'an 'yan sanda a kasar Malaysia suka tare wasu manya hanyoyi a Kuala Lumpur babban birnin kasar, gabanin fara wani gangami da masu rajin kare demukradiya suka shirya.
An dai shirya yin zanga-zanga kan kiraye-kirayen da ake ta yi ga Firaiministan kasar Najib Razak ya yi murabus kan zargin da ake masa da hannu a wata badakala ta makuden kudade.
Ya kuma musanta zargin, sai dai masu fafutika a kasar sun ce yana yiwa masu sukarsa bazarana.