Cuba: Ana zaman makokin mutuwar Fidel Castro

Fidel Castro ya jagoranci juyin-juya-halin da jam'iiyar Communist ta yi a Cuba a 1959

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Fidel Castro ya jagoranci juyin-juya-halin da jam'iiyar Communist ta yi a Cuba a 1959

Hukumomi a kasar Cuba sun ayyana zaman makokin kwana 9 don jimamin mutuwar tsohon shugaban kasar Fidel Castro wanda ya rasu yana da shekara 90.

Za'a kona gawar sa a wani karamin biki a Havana yayin da a mako mai zuwa za'a zagaya da tokar sa zuwa sassa daban-daban na kasar kafin a binne tokar a birnin Santiago dake kudu maso gabashin kasar ranar 4 ga watan Disamba.

Fidel Castro ya shugabanci Cuba a matsayin kasa mai bin jam'iyya daya tsawon kusan shekara 50 kafin dan uwansa Raul ya karbi mulki a shekarar 2006.

Masu goyon bayansa sun ce ya bauta wa al'umar kasar Cuba.

Sai dai ana zarginsa da murkushe 'yan adawa.

'Cuba za ta ci gaba da yin nasara'

Raul Castro ya kammala jawabinsa da yin wani take na juyin-juya hali, inda ya ce: "Nasara tamu ce, kodayaushe!"

Fidel Castro ya dade da fita daga harkokin siyasa, idan aka cire wasu 'yan kalamai da yake yi a jaridun kasar.

A watan Afrilu, Fidel Castro ya yi wani jawabi da ba a cika ganin irin sa ba ranar da ake kammala babban taron jam'iyarsa ta Communist Party.

Ya yi tsokaci kan yadda girma ya zo masa, yana mai cewa duk da haka 'yan kasar Cuba za su ci gaba da yin nasara.

Bayanan bidiyo,

Fidel Castro made a rare appearance at Cuba's Communist Party congress

Castro - wanda ya tsallake yunkurin kisan da aka yi a kansa sau da dama - shi ne shugaban da ba Basarake ba ya fi dadewa a kan mulki a karni na 20.

Wasu fitattun ranaku a rayuwar Fidel Castro

Asalin hoton, AFP/Getty Images

  • 1926: An haife shi a Oriente, lardin da ke yamma maso gabashin Cuba
  • 1953: An daure shi bayan ya jagoranci wani yunkurin tumubuke gwamnatin Batista da bai yi nasara ba
  • 1955: An sake shi daga gidan yari bayan an yi masa afuwa
  • 1956: Shi da Che Guevara suka fara yakin sari-ka-noke
  • 1959: Ya kayar da Batista, inda ya zama Firai Ministan Cuba
  • 1961: Ya yaki mamayar da kungiyar Bay of Pigs, wacce CIA ke mara wa baya
  • 1962: Ya tayar da jijiyoyin wuya kan makamai masu linzami bayan ya amince cewa tsohuwar tarayyar Sobiat za ta iya aikewa da makaman zuwa Cuba
  • 1976: Majalisar dokokin Cuba ta zabe shi a matsayin shugaban kasa
  • 1992: Ya cimma jarjejeniya da Amurka kan 'yan gudun hijirar Cuba
  • 2006: Ya sauka daga shugabancin kasar saboda rashin koshin lafiya