Amurka:Trump ya yi raddi ga neman sake ƙidaya ƙuri'u

Asalin hoton, AFP
Mr Trump ya lashe zabe a jihar Wisconsin ne da 'yar karamar tazara
Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana bukatar neman a sake ƙidaya ƙuri'u na zaben shugaban kasa a jihar Wisconsin a matsayin damfara.
Ya ce hatta abokiyar takarar sa Hillary Clinton ta amince da shan kaye a zaben.
Shi dai Mr Trump ya lashe zabe a jihar Wisconsin ne da 'yar karamar tazara, sai dai jam'iyyar Green Party ta mika bukata a hukumance da a sake bin kadin ƙuri'un don tantance ko akwai alamun tafka magudi.
Mr Trump ya ce shugabar jam'iyyar Jill Stein tana kokari ne kawai ta mayar da kudaden da ta kashe a lokacin yakin neman zabe bisa fakewa da neman gudummuwa don sake ƙidaya ƙuri'un.
Jam'iyyar dai ta na fatan cewa, matakin da ta dauka zai iya zaburar da neman a sake ƙidaya ƙuri'un a jihohin Pennsylvania da Michigan.
Sai dai wani mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Hilary Clinton ya ce zasu shiga cikin ƙidaya ƙuri'un matukar idan aka fara yin hakan.
A bangare guda kuma wasu masana na ganin soke daukacin sakamakon zaben a jihohin uku tamkar abu ne da kamar wuya.