Hikayata 2016: Labarin Ilimi Linzamin Rayuwa

Hikayata 2016: Labarin Ilimi Linzamin Rayuwa

A ci gaba da karanto muku gajerun labaran da suka yi rawar-gani a gasar BBC Hausa ta farko ta rubutun kagaggen labari ta mata zalla, a wannan makon za mu fara kawo muku karatun labarai 12 da alkalan gasar suka ce sun cancanci yabo.

A yau za mu karanto muku labarin "Ilimi Linzamin Rayuwa" na Suwaiba Abdullahi, Dogon Daji, Sakkwato.