Dan takarar APC ya lashe zaben gwamnan Ondo

APC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yanzu jiha daya ce kawai APC ba ta mulki a kudu maso yammacin Nigeria

Hukumar zaben Najeriya ta ayyana dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da aka yi ranar Asabar.

Rotimi Akeredolu ya samu kuri'a 244, 842, yayin da mutumin da ke biye masa, dan takara a karkashin jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede ya lashe kuri'a 150,380.

Babban baturen zaben jihar Farfesa Ganiyu Ambali, wanda ya bayar da sakamakon zaben, ya kara da cewa mutum 1,647, 976 ne suka kada kuri'unsu.

Sai dai jam'iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben, tana mai zargin hukumar zabe da hada baki da jam'iyyar APC wajen yin magudi.

Rotimi Akeredolu zai karbi mulki ne daga hannun Olusegun Mimiko na jam'iyyar PDP, wanda ya kwashe shekara takwas a kan mulki.

Zaben na jihar Ondo ya ja hankalin 'yan Najeriya sakamakon kai ruwa ranan da aka rika yi tsakanin jiga-jigan manyan jam'iyyun biyu da ma masu son tsayawa jam'iyyun takara gabaninsa.

Yanzu dai jiha daya ce kadai ta rage a hannun jam'iyyar da ba APC ba a yankin kudu maso yammacin Najeriya, wato jihar Ekiti.