FA na bincike kan yin lalata da 'yan wasa

'Yan wasa David White, Andy Woodward, Steve Walters da kuma Paul Stewart sun shaida wa BBC cewa an yi lalata da su

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

'Yan wasa David White, Andy Woodward, Steve Walters da kuma Paul Stewart sun shaida wa BBC cewa an yi lalata da su

Hukumar kwallon kafar Ingila, FA ta tabbatar cewa tana gudanar da bincike kan zarge-zargen yin lalata da 'yan wasa.

Tsofaffin 'yan kwallon kafa da dama ne suka fito fili suka ce koci-koci sun yi lalata da su a lokacin da suke matasan 'yan wasa.

'Yan sanda hudu ne ke gudanar da bincike kan zarge-zargen kuma tuni mutum sama da 100 suka mika korafinsu ta layin wayar da aka bude domin yin hakan.

FA ta ce tana aiki tare da 'yan sanda a kan batun, tana mai karawa da cewa dole "mu tabbatar ba mu yi wani abu da zai yi karan-tsaye ga tsarin kama masu laifi ba".

Hukumar ta bayar da umarni ga kamfanin lauyoyi na Kate Gallafent QC, wanda ya kware wajen kare hakkin yara kanana, ya taimaka wajen gano masu laifi.

An samar da layin waya kan batun ne bayan tsofaffin 'yan wasa David White, Andy Woodward, Steve Walters da kuma Paul Stewart sun fito fili sun bayyana yadda aka yi lalata da su.