Nigeria: Izala na goyon bayan dokar wa'azi amma...

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce kungiyar Izala tana daukar matakai wajen yin gyara a harkokin wa'azi
Bayanan hoto,

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce kungiyar Izala tana daukar matakai wajen yin gyara a harkokin wa'azi

A Nigeria, wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci a ƙasar, sun fara tsokaci game da shirin dokar ƙayyade wa'azi da wasu jihohin kasar ke shirin zartarwa.

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah wa ikamatussunnah ta ce dokar ba za ta yi tasiri ba har sai an dorawa ƙungiyoyin addinin nauyin saka wa masu wa'azinsu ƙa'ida da kansu.

Tun ba yau ba ne dai ake zargin masu wa'azin addini a kasar da cusa wa mabiyansu aƙidu masu tsauri ko kuma ingiza wutar rikici tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Hakan ya sa wasu jihohi suka fara yunkurin bullo da dokokin takaita ayyukan masu wa'azin.