Nigeria: 'Yan gudun hijira na bukatar taimako

Sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mata da kananan yara da tsofaffi ne suka fi shan wahala, a yakin da ake yi da mayakan Boko Haram

Kungiyoyi da dama na ci gaba da yunkurin tallafa wa 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, a Najeriya.

Duk da irin nasarorin da dakarun kasar da na makwabtan kasashe suka samu na kwace yawancin garuruwa da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suke rike da su a baya, har yanzu, mafiya yawan wadanda abin ya shafa na zaune ne a sansanoni daban-daban da hukumomi suka kafa.

A yanzu haka kuma 'yan gudun hijrar na ci gaba da kokawa kan halin kuncin da suke ciki.

A karshen mako ne dai wata tawagar kungiyar matan sojijin sama na Najeriya, ta kai ziyara ga 'yan gudun hijira da ke sansanin garin Bama a jihar Borno.

Ziyarar ta kunshi kai tallafin kayan abinci da na bukatun yau da kullum ga 'yan gudun hijirar.

Bayanan hoto,

Matan sojojin sama na raba wa 'yan gudun hijra tallafi

Kimanin mutane dubu goma sha uku ne dai ke zaune a sansanin 'yan gudun hijirar na Bama.

Editan sashen Hausa na BBC, Nazir Mika'il wanda ya kasance tare da tawagar ya rawaito cewa yara kanana da mata da tsafoffi ke ta sowa da murna a lokacin da tawagar ta isa da kayan tallafin.

Wata babbar matsala da 'yan gudun hijirar ke fama da ita baya ga ta abinci, ita ce rashin isasshen makewayi.

Har wa yau, akwai jama'ar da ke kwana a sararin Allah ko dan tantin da ake kafawa ba su samu ba.

Fatan mutanen dai shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali su dore a Nigeria, a kuma kawo karshen tada kayar baya ta kungiyar Boko Haram.

Hakan ne dai zai ba su damar komawa gidajensu, domin gaba da rayuwa kamar yadda aka saba a baya.

Tun a watan Maris din shekarar 2015 ne dakarun Nigeria suka yi ikrarin fatattakar mayakan Boko Haram daga garin na Bama.

Sai dai har yanzu jama'ar da suka yi gudun hijira ba su samu damar komawa gidajen su ba.

Abin tambayar a nan shi ne ko za a dore wajen ci gaba da kai wa mutanen kayan agaji?

Bayanan hoto,

Layin 'yan gudun hijra wajen karbar tallafi

Bayanan hoto,

Sojoji na kokarin kange masu son yin wawa a wajen rabon tallafin