Za mu je kotu kan zaben Ondo — PDP

PDP
Bayanan hoto,

Jam'iyyar PDP ta zama mai adawa a Najeriya

Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, ta ce za ta garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben jihar Ondo da Hukumar zaben kasar ta bayyana wanda ya ba wa jam'iyyar APC mai mulki nasara.

Hukumar zaben kasar dai wato INEC, ta ce, dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Rotimi Akeredelu ne ya lashe zaben, bayan kayar da dan takarar PDP, Eyitayo Jegede.

Mai ba wa shugaban jam'iyyar PDP shawara kan yada labaru, Barrister Abdullahi Jalo, a hira da BBC, ya yi zargin tafka magudi, a inda ya ce dole ne su je kotu domin neman hakkinsu.

Sai dai kuma a nata martani, jam'iyyar APC, ta bakin mataimakin shugaban jam'iyar na kasa yankin arewacin Najeriya, Senator Lawal Shu'aibu, ta ce zafin kaye ne ya sa 'ya'yan jam'iyyar ta PDP kin amincewa da sakamakon zaben.

Dama dai jam'iyyar ta PDP, ta fitar da wata sanarwa da safiyar Litinin, a inda ta yi watsi da sakamakon zaben.

Ta kuma zargi hukumar zabe ta INEC da hada baki da APC wajen murde zaben jihar ta Ondo.