China ta ce ta ga ribar haihuwa fiye da ɗaya

Tsofaffi ne suka fi yawa a China saboda dokar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

A baya dai China ta takaita haihuwar 'ya'ya fiye da daya

Gwamnatin kasar Sin wato China ta fitar da takarda da ke nuna gamsuwarta da sabon tsarin da kasar ta fito da shi na bai wa ma'aurata damar haihuwar yara biyu maimakon daya.

Sakamakon wannan sabon tsarin dai, za a iya haihuwar yara miliyan 17 da rabi a 2016, abin da ke nuni da cewa za a sami sabbin jini a kasar.

Hakan na nufin an samu karin kaso 5.7 daga 2015.

Gwamnatin kasar ta China dai ta sassauta dokar hana haihuwa fiye da ɗa daya ne sakamakon karuwa tsaffi da ake samu a kasar.

Sannan kuma a ba wa ma'aurata da suke a birni haihuwar yara biyu.

Sai dai kuma iyaye da yawa a kasar na korafin cewa ba su da halin da za su iya biya wa ɗansu na biyu kudin karatu.