'Yan sandan na binciken hari a jami'ar Ohio

'Yan sanda a Amurka
Bayanan hoto,

'Yan sanda a Amurka

'Yan sandan a Amurka sun ce suna gudanar da bincike akan ko farmakin da wani dalibi a jami'ar Ohio ya kai, hari ne na ta'addanci.

Mutane tara ne dai suka jikkata lokacin da Abdul Razak Ali Artan, dan asalin kasar Somaliya ya abka da wata mota cikin taron jama'a wadanda ke tafiya a kasa, kafin daga bisani ya fito daga cikin motar ya rika kaiwa masu wuce wa hari da wuka.

Wani dan sanda dake kusa da wurin dai ya harbe mutumin har lahira, sai dai jami'ar da yake karatu ta ce a yanzu ta dage haramcin da aka sanya a harabar jami'ar.

Kawo yanzu dai wadanda suka jikkata na samun sauki a asibiti.