Korea ta Kudu: Shugaba Park ta ce a shirye take ta yi murabus

Asalin hoton, EPA
Shugabar kasar na fuskantar matsin lamba
Shugabar kasar Korea ta Kudu Park Geun-hye ta bukaci majalisar dokoki da su taimaka mata wajen gano hanyar da za ta yi murabus.
Ms Park ta fuskanci kiraye-kirayen ta yi murabus, a yayin da ake gudanar da bincike kan ko ta kyale aminiyarta amfani da damar da take da ita wajen samun abubuwa na kashin kanta.
Ta ce za ta bar wa majalisar dokoki wuka da nama kan makomarta da ta hada da gajarta wa'adinta, amma ba ta son ta sauka ba tare da an cike gibi ba.
A ranar Jumma'a ne ake sa ran majalisar dokokin za ta yi zaman tattaunawa kan ko Ms Park din za ta fuskanci tsigewa.
Wasu 'ya'yan jam'iyya mai mulki sun ce ya kamata shugabar ta sauka daga mukaminta cikin ruwan sanyi kafin a kai ga tsige ta.
Jam'iyyun siyasa na zarginta da kokarin kaucewa tsigewa.
A baya dai Ms Park ta nemi afuwa, ta kuma ce ''ranta ya baci'' kan rudanin siyasar da ya dabaibayeta, amma ta ki ta yi murabus.

Asalin hoton, EPA
Dubban masu zanga-zanga ne suka bukaci shugabar da ta yi murabus
Badakalar ta fara ne kan dangantakar shugabar kasar da kawarta ta kud-da-kud Choi Soon-sil.
An zargi Ms Choi da kokarin karbar makudan kudade daga kamfanonin Korea ta Kudu.
Har ila yau ana zarginta da amfani da kawancenta da Ms Park wajen nema wa kanta kwangiloli.
Akwai kuma zargin cewa Ms Park ta bai wa Ms Chois muhimman takardun sirri na gwamnati ta hannun wani mai bata shawara.
Ms Choi na tsare a hannun 'yan sanda, inda take fuskantar tuhume-tuhume.