An fara shirye-shiryen nada sabon sarki a Thailand

Thailand Yarima mai jiran gado Maha Vajiralongkorn

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

A fadin kasar ta Thailand dai yariman ne ake sa ran zai gaji mahaifinsa

KasarThailand ta fara shirye-shirye nada Yarima mai jiran gado Maha Vajiralongkorn a matsayin sabon sarkin.

Majalisar dokokin kasar ta amince da aikewa da takardar gayyata a hukumance, da zai amince kafin ya hau kan karagar mulkin.

Sarki Bhumibol Adulyadej da ake tsananin kauna ya mutu ne a ranar 13 ga watan Oktoba, da ya jefa kasar ta Thailand cikin jimami.

A fadin kasar dai yariman ne ake sa ran zai gaji mahaifinsa, amma a baya hukumomi sun bayyana cewa ya na so ya daga zuwa akalla shekara guda.

Dalilan da aka bayar a hukumance sune suna son bai wa 'yan kasar damar yin zaman makoki da alhinin rasuwar baban shi kafin ya zama sarkin.

A baya dai mahukunta na nuna shakku kan yadda yarima mai jiran gado zai iya rike karagar mulkin da mahaifinsa ya zauna a kai har na tsawon shekaru 70.

Sarautar na da muhimmin gurbi a jerin matsayi a siyasar kasar ta Thailand.

Sarki Bhumibol Adulyadej ya kasance gagarabadau a lokacin tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa da suka hada da lokacin juyin mulkin da sojiji suka yi a shekara ta 2014.

Nan da 'yan kwanaki ne 'yan majalisar dokokin za su gana da Yarima mai jiran gadon don yi masa gayyata a hukumance.