Bamu amince Zuma ya sauka daga mulki ba- ANC

Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jam'iyar ANC bata amince shugaba Zuma ya sauka daga mulki ba

Shugabannin jam'iyyar dake mulki a Afirka ta Kudu, jam'iyar ANC ta yi watsi da wani kira da aka yi na Jacob Zuma ya sauka daga mulki.

An tattauna shawarar, wadda daya daga cikin ministocinsa suka bayar wajan wani taron shugabanninta wanda wani jami'in jam'iyyar yace an yi shi cikin armashi da gaskiya a wani lokacin kuma ya yi zafi.

Wa'adin mulkin shugaba Zuma dai ya yi rauni kan zarge zargen cin hanci da kuma zargin hada kai da wasu 'yan India attajirai da ya kira abokansa.

Wannan ba shine karon farko da shugaban ke fuskantar kalubalan neman tsige shi daga mulki ba. Da safiyar ranar Talata ne shugaba Zuma ya tafi Cuba domin halartar jana'izar Fidel Castro.