Abubakar ya karbi kyauta ta adabi ta Naira miliyan 40

Abubakar Adamu tare da mai dakinshi da ministan yada labarai na Najeriya, Lai Muhammad da shugabannin kamfanin NNPC
Bayanan hoto,

Abubakar Adam dan jarida kuma marubuci ne

A ranar Litinin din nan ce marubucin nan kuma dan jarida, Abubakar Adam Ibrahim, ya karbi kyautar adabi ta Najeriya ta kamfanin NLNG ta 2016.

Kyautar dai ta kai Naira miliyan 40, kuma an mika wa marubucin cakin kudin ne a wurin wani taro na musamman da aka gudanar a Abuja.

Mahaifiyar Abubakar, Hajiya Hauwa, da mai dakinsa, Maryam, na cikin 'yan uwa da abokan arzikin da suka halarci bikin.

A watan da ya gabata ne dai aka bayyana Littafin "Season of Crimson Blossoms" na marubucin a matsayin wanda ya lashe kyautar.

Sauran littattafan da Season of Crimson Blossoms ya yi takara da su su ne "Born on a Tuesday" na Elnathan John, da "Night Dancer" na Chika Unigwe.

Littafin na "Season of Crimson Blossoms" ya yi magana ne a kan wani nau'i na soyayya da ba kasafai ake ganin irinsa ba, musamman a arewacin Najeriya, inda wata baiwar Allah da ta manyanta ta ke soyayya da wani matashi da ya shiga gidanta da nufin sata.