Mai cutar gilu ta zama gwarzuwa

Isabella Springmuhl

Asalin hoton, JUAN CARLOS MENENDEZ

Bayanan hoto,

shekarar Isabella 19 kuma har ta nuna irin bajintarta a makon ƙawa da ake yi birnin london

Ga wata mata mai fama da cutar gilu, ƙyama da nuna wariya na daya daga cikin abubuwan da ta fuskanta har ma a makon taron kayan ƙawa da ake yi a birnin London. Yanzu wannan matar mai yi tare da samar da kayan sakawa daga Guatemala, tana daya daga cikin jerin sunaye 100 na BBC na mata masu Ilhama.

Kafin duniya ta gano ta a matsayin mai dinki tare da tsara tufafi, Isabella Springmuhl ta ce makarantun kawa biyu ne suka ki karbar ta a garin Guatemala inda nan ne garinta saboda tana fama da rashin lafiyar gilu.

"Sun ce ba zan iya jurewa ba, " kamar yadda mai shekara 19 ta tuna.

Asalin hoton, JUAN CARLOS MENENDEZ

Bayanan hoto,

Isabella ta fara samar da tufafin mutane bayan ta koyi dinka kayan yatsana

Amma kuma kin amincewar da makarantun suka yi ne ya bai wa Isabella kwarin gwiwan fuskantar wani sabon babi a rayuwarta a cewar mahaifiyarta Isabel Tejada.Ga wata mata mai fama da cutar gilu, kema da nuna wariya na daya daga cikin abubuwan da ta fuskanta har ma a makon taron kayan kawa da ake yi a birnin London.

" Rai na ya matukar baci saboda wadannan makaratun sunki su bai wa Isabella damar koyo. Abin tausayi ne, amma kuma hakan ya sa ta canza komai. A lokacin ta yanke shawarar tana so ta koyi dinki saboda haka sai na kai ta makarantar koyon dinki na mata.

Asalin hoton, JUAN CARLOS MENENDEZ

Bayanan hoto,

Isabella ta fara samar da yatsana da girmansu ya kai kananan yara

A yayinda take koyon dinkin, sai aka ce Isabella ta rika dinkawa 'ya tsana tufafi, irin 'yatsanar da ake samarwa daga Guatamela da al'adar Mexico. A kan saka 'yatsanonin a karkashin matshin yara da fatan cewar zai debe musu duk wata damuwa da kewa dake tare da su a yayinda suke baci.

Isabella ta sauya sallo

" A cewar Mrs Tejada, " Isabella bata so ta rika dinka wa 'ya tsanonin kaya. " Sai ta fara samar da yatsanonin da girman su ya kai kamar girman kananan yara kuma sai take saka musu tufafi masu sirfani da kuma launuka daban-daban wanda yanzu aka santa da shi.

Sabella ta bar dinka kayan 'yatsana ta koma tsara tare da dinka kayan mutane kuma ba da jimawa ba ta samar da kaya masu yawa wanda ya ja hanakalin masu harkar kayan kawa a duniya.

Asalin hoton, JUAN CARLOS MENENDEZ

Bayanan hoto,

Dangi tare da abokan Isabella sun nuna mata so tare da goyon baya a lokacin da aka kyamace ta

Ire-iren tufafin da Isabella ta ke samar wa wajen yin amfani da yadikan Gautemala tare da surfani da launuka daban-daban ya sa an gano matashiyar mai yin tufafi wace aka riga aka gayyace wajen bikin kayan kawa da za a yi a kasar Panama da garin Miami a shekara mai zuwa.

"An nuna min wariya.

Asalin hoton, ALEXS VAZQUEZ

Bayanan hoto,

Isabella ta nuna irin tufafin da take samarwa a makon kayan kawa a birnin London

Asalin hoton, ALEXS VAZQUEZ

Bayanan hoto,

Babban burin Isabella shine a san ta da aikinta

" Amma dangina da abokai sun nuna min so wanda ya taimaka min na cimma buri na. Na riga naje birnin Rome da London, da Mexico kuma an gayyace zuwa Miami da Chicago da kuma mai yiwuwa Paris.

Ina so mutane su sanni a kan aiki na da kuma abinda ke cikin zuciya.