Gaskiya ne abokantakar da ake faɗa ta fi daɗi?

Wace ta fito a littafin nan mai suna The Girl on Train

Asalin hoton, KATE NEIL

Bayanan hoto,

Ba kasafai mata ke kwance tsakaninsu da Allah ba

Paula Hawkins, shaharriyar marubuciyar litaffin nan mai suna The Girl on the Train, ta ce ba a ko da yaushe kawance tsakanin mata ke zamantowa ana yin sai tsakani da Allah ba amma kuma a wasu lokutan ya kan kasance da dadi.

Ni da kawata ta kut-da-kut mun samu matsala a lokuta da dama a lokacin muna cikin shekara 20 da haihuwa. Mun yi fada kuma muka bar yi wa juna magana sai dai mun rika kewar juna daga baya kuma muka dawo tare muka ci gaba da kawancenmu.

Ba mu yi fada a kan maza ba, ba mu taba fada kan wani abin tayar da hanakli ba. Fadanmu a kan abubuwa masu muhimmanci ne kama daga siyasa, dangi, kasancewa uwa, da kuma irin zabin da muka yi wa kanmu. Da kuma irin kurakuran da muka yi.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

A lokuta da dama kawance mata na cike da sarkakaiya

Mun rabu amma kuma mun dawo tare. Mun taimaka wa juna kuma mun goyi bayan juna. Mun kasance masu bai wa juna karfin gwiwa a lokutan da bukatar hakan ta taso. Abin da sarkakiya. Har yanzu ma a wasu lokutan akwai sarkakiya.

'Kawancen mata mai cike da sarkakiya'

Ga yadda labarin ya kasance: Maza suna abota tsakaninsu da Allah bata tare da sarkakiya ba amma mata daban suke. Dangantakar tsakanin mata kan haifar da sabani da gasa tare da kisihi da kuma rashin aminci.

A lokuta da dama idan mata sukan ki amincewa da wasu sauyi da suke fuskanta a rayuwarsu ana samun bambamce bambamce a ra'ayoyinsu. Ana ganinsu a matsayin masu yawan fada ko a ja gashi, ko ayi muntsini wanda ba kasafai maza ke tsintar kansu cikin irin yanayin ba.

Akwai abubuwa kadan na jin dadi a lokacin da mutum ke manyata amma a nan a ra'ayi na abubuwa biyu ne.

Asalin hoton, KATE NEIL

Bayanan hoto,

Maza suna abota tsakaninsu da Allah

Na farko dai babu namijin da zai rika yi wa mace wace ta manyata irin kiran da suka saba yi wa 'yan mata a kan titi.

Na biyu kuma ana yin kawance cikin sauki.

Ana samun raguwa a naci wajen zaben abu kuma ana kana iya yin irin kawance da kake so. Ba lalai bane su kasance masu sauki, amma kuma me yasa zasu kasance masu saukin? Me yasa ba a iya kawance kut-da-kut kuma mai kunshe da abubuwan da suka danganci alaka daba-daban kamar alaka tsakanin masoya.