BH: Ina da ja kan yawan mutanen da suka mutu — Shettima

Ya kara da cewa an yi asarar biliyoyin daloli a yankin Arewa maso gabas
Bayanan hoto,

Kashim Shettima ya ce neman tallafi ne a gabanmu

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce, ko kadan ba dai-dai ba ne ace mutanen da suka mutu a shiyyar Arewa maso gabashin kasar sakamakon ayyukan Boko Haram, daga shekarar 2009 kawo lokacin da aka bayar da kididdigar, dubu 10 ne.

A watan maris din da ya gabata ne dai shugaba Muhammadu Buhari, ya ce 'yan kasar kimanin dubu 10 ne suka rasu sakamakon rikicin na 'yan kungiyar Boko Haram, tun daga shekara ta 2009.

Gwamna Kashim Shettima, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Abuja, ya kuma ce an yi hasarar kadarori a yankin na kusan dala biliyan tara.

"A jihar Borno kadai an kona azuzuwa dubu 5335, an kona makarantun sakandare guda 38 sannan gidajen mutane dubu 956,453 aka kona." In ji Shettima.

Sai dai kuma gwamnan ya ce, yanzu ba lokacin ja-in-ja ba ne kan adadin mutanen da suka mutu.

Ya kara da cewa abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, shi ne, yadda za a tallafawa mutanen da rikicin ya dai-daita.

Kashim Shettima ya kuma bayyana irin karfin gwaiwar da yake da shi wajen samun tallafin musamman a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Sharhi, Usman Minjibir

Kusan za a iya cewa har kawo yanzu babu wata kididdiga da wani zai iya bugar kirji ya ce ita ce sahihiya kan adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar rikicin Boko Haram.

Ko da Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama sun sha samun karo wajen fitar da alkaluma tsakaninsu da bangarorin gwamnati musamman ma jami'an tsaro.

A shekarar 2014, sai da Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa an kashe mutane sau fiye da biyar din kididdigar da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta bayar a shekarar.

A lokacin dai gwamnatin shugaba Jonathan ta ce mutane fiye da dubu 11 ne suka mutu tun daga 2009 lokacin da hare-haren kungiyar ya fara ta'azzara.

Sai dai kuma mafi yawancin lokaci, a kan kasa tantance mutanen da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suka kashe da kuma wadanda ake zargin jami'an tsaron kasar da kisa.