'Ya kamata Donald Trump ya yi takatsantsan'

Mista Trump na son inganta alaka da Russia
Bayanan hoto,

Donald Trump ya ce zai wargaza yarjejeniyar da ta sanya Amurka ta kwaye wa Iran takunkumi

Daraktan hukumar Leke Asiri ta Amurka wato CIA, John Brennan, ya ja kunnen zababben shugaban Amurka, Donald Trump, kan kasar Iran.

Mista Brennan ya ce ka da mista Trump ya kuskura ya dawo da hannun agogo baya dangane da yarjejeniyar da ta sanya Amurka ta kwaye wa Iran takunkumi kan shirinta na samar da makamin nukiliya.

Donald Trump dai ya yi furucin cewa zai wargaza yarjejeniyar, a lokacin kamfe dinsa.

A wata hira da wakilin BBC, John Brennan ya kuma ce kara da cewa dole ne gwamnatin Trump ta yi takatsantsan wajen kulla alaka da Rasha.

Har wa yau, mista Brennan ya ja hankalin mista Trump da 'yan tawagarsa da ka da su rusa tsare-tsaren da Obama ya dora kasar a kai.

Darektan na CIA ya kuma soki azabtar da mutane da ruwa lokacin tambayoyi da jami'an tsaro ke yi wa wadanda ake tuhuma.