Za a yi gwajin sabon maganin HIV a Afirka ta kudu

Tambarin HIV

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a fitar da sakamakon gwajin a 2020

A ranar Labara ne za a gwada wani sabon maganin cutar HIV a kasar Afirka ta kudu wacce ke cikin kasashe na gaba-gaba wajen masu fama da cutar a duniya.

Masana kimiyya sun ce gwajin shi ne mafi girma da zurfi da za a yi a kasar.

Kimamin mutum miliyan bakwai ne a Afirka ta kudu ke dauke da cutar, yayin da mutum dubu daya ke kamuwa da ita a kullum.

Masana daga Amurka, wacce ke daukar nauyin gwajin, sun ce suna fatan gwajin shi ne na karshe da zai zama silar gano maganin cutar kwata-kwata.

Za a yi gwajin ne bayan an yi irin sa a kasar Thailand a shekarar 2009, wacce a yanzu take da kashi 30 na garkuwa ta kamuwa da cutar.

Ana sa ran za a fitar da sakamakon gwajin nan da shekara hudu masu zuwa.