Za a shiga bala'i idan aka soke yarjejeniyar Iran - Shugaban CIA

John Brennan
Bayanan hoto,

John Brennan zai bar mulki a watan Janairu

Daraktan hukumar leken asirin Amurka CIA ya gargadi shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump kan alwashin da ya sha na soke yarjejeniyar da aka kulla da Iran game da makamashinta na nukiliya, yana mai cewa yin hakan zai zama "babban bala'i da wauta."

A wata hira da ya yi da BBC, John Brennan ya kuma bai wa sabon shugaban kasar shawara da ya yi takatsantsan da alkawuran da Rasha ta yi masa, yana mai dora alhakin masifar da ke faruwa a Syria kan Rashar.

A lokacin yakin neman zabensa, Mr Trump ya yi barzanar soke yarjejeniyar da aka kulla da Iran sannan ya ce zai rika yin alaka ta kut-da-kut da Rasha.

Mr Brennan dai zai sauka daga kan mukaminsa a watan Janairu bayan ya kwashe shekara hudu yana jagorancin CIA.

A hirar, wacce ita ce ta farko da ya yi da wata kafar watsa labarai ta Birtaniya, John Brennan ya shata hanyoyi hudu da ya ce dole sabuwar gwamnati ta yi kaffa-kaffa wajen daukar mataki a kansu.

Cikin su har da irin kalaman da za a rika amfani da su a kan yaki da ta'addanci, da dangantakar Amurka da Rasha, da yarjejeniyar makamashin nukiliya da aka kulla da Iran da kuma hanyoyin da za a yi amfani da mutanen da CIA ta lallaba suka daina tayar da kayar-baya.

Rawar da Rasha ke takawa a yakin Syria

Mr Brennan ya ce babu wani fata na gari game da yakin da ake yi a Syria, yana mai dora alhakin kashe-kashen da ake yi a kasar kan gwamnatin Syria da ta Rasha.

Gwamnatin Barack Obama dai ta dauki matakin bayar da goyon baya ga masu sassaucin ra'ayi da ke yaki da gwamnatin Basharul-Assad.

Daraktan na CIA ya ce ya yi amannar cewa ya kamata Amurka ta ci gaba da bin wannan hanya domin hana "kisan babu gaira babu dalilin" da gwamnatin Syira da Rasha da kuma kungiyar Hezbullah ke yi wa 'yan kasar.

Asalin hoton, AFP

Satar bayanai kan zaben Amurka

Daraktan na CIA ya tabbatar da cewa Rasha ta nemi satar bayanai domin taimakawa kan zaben kasar Amurka da aka yi a watan jiya, sai dai ya kara da cewa hakan bai yi wani tasiri ba.

Ya ce sau da dama ya yi magana da takwaransa na Rasha inda ya soke shi kan wannan yunkuri, yana mai gargadinsa cewa Amurka za ta iya rama duk abin da aka yi mata.

Yarjejeniyar da aka kulla da Iran

Ya kuma gargadi Donald Trump kan matsayinsa a lokacin yakin neman zabe cewa zai warware yarjejeniyar da aka kulla da Iran kan makamashin nukiliyarta.

Mr Brennan ya shaida wa BBC cewa, "Ina tsammani soke yarjejeniyar zai zama wani babban bala'i."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

John Brennan ya gargadi Trump da kada ya yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla da Iran

Ya ce, "Da farko ma ya kamata a sani cewa babu wata gwamnati mai shigowa da ta soke yarjejeniyar da gwamnatin da ta gabace ta ta kulla, don haka wannan ne zai zama karon farko."

A cewarsa, hakan zai karfafa gwiwar masu tsattsauran ra'ayi a Iran sannan ya sa wasu kasashen su fara shirin samar da makaman nukiliya.

Barazanar ta'addanci

Yaki da ta'addanci shi ne babban batun da aka fi bai wa muhimmanci.

Daraktan na CIA ya ce kungiyar IS na kan bakanta na ci gaba da kai hare-hare, yana mai cewa duk da koma-bayan da take samu a fagen yaki har yanzu tana da karfin kaddamar da hare-hare a kasashen yammacin duniya.

Jirage marasa matuka da kuma kulle 'yan ta'adda

An dora nauyin samar da bayanan sirri kan CIA, don haka yawancin ayyukanta na boye ne.

Sai dai daya daga cikin manyan kalubalen da John Brennan ya fuskanta a baya bayan nan shi ne yadda CIA ke azabtar da mutanen da ake tsare da su ta yin amfani da ruwa wajen toshe kafofin numfashinsu tun bayan harin 9/11.

Asalin hoton, Getty Images

Donald Trump ya ce zai dawo da yin amfani da wannan hanya idan hakan ne zai zama mafita.

Sai dai John Brennan ya bayyana karara cewa yin hakan zai zama kuskure.

'Yaki da Musulinci'

Darakntan CIA ya ce har yanzu bai tattauna da jami'an sabuwar gwamnati kan 'yaki da Musulunci' ba, amma a shirye yake ya tattauna da su.

Ya ce, "Akwai mutane da dama da ke karanta jaridu ko sauraren rediyo inda ake ba su labaran kanzon-kurege. Don haka zan so sabuwar gwamnati ta fahimci gaskiyar al'amari. Kuma ya rage ruwansu su dauki nauyin abubuwan da za su faru."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Michael Flynn a wajen gangamin yakin neman zaben jam'iyyar Republican

Wasu daga cikin mambobin sabuwar gwamnati irin su Janar Michael Flynn, sun sha cewa ya kamata Amurka ta fahimci cewa tana yakin cacar-baka ne da Musulmi 'yan ta'adda.

Sai dai da aka tambaye shi ko yin amfani da kalmar "yakin cacar-baka" yana da kyau, sai shugaban na CIA ya ce ya kamata sabuwar gwamnati "ta samu horo" kan kalamai da sakonnin da za ta rika aikewa da su.

Ya kara da cewa kin yin hakan zai sa 'yan ta'adda su ga cewa gwamnatin ba ta kaunar Musulmi.