Za a karrama Belgium saboda iya yin barasa

giya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kasashen duniya da dama na son shan giyar Belgium

Hukumar raya ala'adu ta majalisar dinkin duniya za ta karrama kasar Belgium saboda kwarewar 'yan kasar wajen yin barasa.

Manyan jami'an hukumar, wadanda za su yi taro a ranar Laraba, za su duba yiwuwar sanya kasar cikin jerin manyan abubuwan tarihi saboda gwanintar da suke da ita wajen iya sarrafa giya.

Idan hakan ya tabbata, Belgium za ta bi jerin fiye da abubuwa 300 da hukumar ta karrama saboda tarihinsu.

Abubuwan sun hada da wasan hawa rakumi da ake yi a Mongolia da wasan rawa a kan almakashi a Peru.

Kasar Belgium tana sarrafa nauyin giya fiye da dubu, wadda ake sha a kasashe daban-daban na duniya.