Al-Bashir ya ce Donald Trump zai yi sauƙin-kai

Shugaba Omar al-Bashir

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Al-Bashir ya ce Donald Trump ba munafiki bane

Shugaban Sudan, Omar al-Bashir ya yabi zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump, yana mai cewa zai fi sauki ya yi mu'amala da shi.

A wata hirar da yayi da jaridar Emirati al-khaleej, Bashir ya ce Mista Trump yana mayar da hankali kan abin da Amurkawa suke so, ba kamar yadda wasu ke mayar da hankali kan dimokuradiyya da 'yancin dan adam da kuma gaskiya ba.

Ya kara da cewa, "Za mu iya mu'amala da munafikai amma a nan mun hadu da mutum mai zuciya daya.

Na tabbatar cewa yin mu'amala da Trump zai fi sauki a kan wasu saboda mutum ne da baya munafunci kuma dan kasuwa ne wanda ke duba abubuwanda wandanda ke hulda da shi ke so, a cewar Mista Bashir.

Shugaban kasar Sudan din ya hau kan mulkin kasar ne a wani juyin mulki a shekarar 1989 kuma tun lokacin ake zarginsa da yin mulkin kama-karya.

Kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya ICC na tuhumar sa da kisan kiyashi a Darfur, kodayake ya sha musanta zargin.