An kama dalibi dan Nigeria da kwayoyi a Mauritius

kwayar heroin

Asalin hoton, Mauritius Broadcasting Corporation

Bayanan hoto,

'Yan Najeriya sun yi kaurin suna wajen safarar miyagun kwayoyi

An kama wani dalibi dan Najeriya a kasar Mauritius bayan an kwace wani abu wanda ake zaton kwayoyi ne da ya kunshe a wasu kananan robobi.

A ranar Talata ne dai 'yan sanda suka kama Uchenna Philips Okafor mai shekara 23 a garin Flic-en-Flac da ke bakin ruwa a lokacin da suke aiki a boye na neman masu laifi.

Har yanzu Mista Okafor, wanda ke zaune a tsibirin Mauritius bai mayar da martani a kan zargin da ake mai na hulda da miyagun kwayoyi ba.

Mista Okafor ya zuba kwayar heroin mai nauyin giram 25 wanda kuma darajarta ta kai dala 103,000 a cikin kananan robobin man shafawa guda 26.

'Yan sanda sun ce hukumar kula da shige da fice da jami'an da ke kula da harkokin miyagun kwayoyi sun dakatar da shi a filin jirgin sama na tsibirin a ranar Lahadi.

An aike wa Mista Okafor sakon ne daga filin jirgin saman Charles de Gaulle da ke kasar Faransa.

'Yan sanda sun ce an kwace kudin Mauritius da na kasar Bangladesh da takardar shaidar zama dan kasa ta bogi na Mauritous daga hannun Okafor.