Mata 100: Yadda Hafsat Abdulwaheed ta kalubalanci gwamna

  • Muhammad Kabir Muhammad
  • BBC Hausa, Abuja

Wai shin me ya sa mata suka fi yawa a cikin marubuta littattafan kagaggun labarai na Hausa? Manazarta da dama dai sun yi bayani cewa hakan na faruwa ne saboda a kasar Hausa ba kasafai mata kan samu damar bayyana abin da ke zuciyarsu a bainar jama'a ba, dalilin da ya sa rubutu ya zama muhimmiyar hanyar sadarwa a gare su. Sai dai wadansu marubutan kan kuma mike tsaye don ganin an kawo sauyi a aikace. Hajiya Hafsat Abdulwaheed, mace ta farko da aka wallafa littafinta na kagaggen labari a harshen Hausa, kuma tana cikin wadanda suka yi irin wannan yunkuri.

Bayanan bidiyo,

Hafsat Abdulwaheed ta rubuta littattafai fiye da 30

Ba ko wacce mace ba ce za ta bugi kirji ta ce za ta yi takarar gwamnan jiha a Najeriya don kawai gwamna mai ci ya kalubalanci mata, duk da cewa ita ba fitacciyar 'yar siyasa ba ce. 'Yan siyasar ma yaya suka kare?

Lokacin da Najeriya ta koma turbar dimokuradiyya a shekarun 1999/2000, Hafsat Abdulwaheed ce ke jagorantar reshen Jihar Zamfara na wata kungiyar kare muradun mata mai suna Baobab. Bayan da shugabannin kungiyar suka ziyarci Jihar daga cikin abubuwan da suka gabatar wa gwamna a wancan lokacin shi ne damuwarsu cewa babu mata a cikin gwamnatinsa.

"Ni ban je [ziyarar] ba", inji marubuciyar, "saboda na san ba zan iya ji in yi shiru ba, ba zan gani in kyale ba.

"Da suka dawo sai suka ce min sun tambaye shi, sai ya ce ai babu mata masu ilimi a Zamfara da za su iya rike wani [mukami a gwamnatin]. Jin haka ni kuma sai na ga muna da mata masu ilimi, ko a gidana kadai ina da 'ya'ya masu karatu—akwai gidaje da yawa da 'ya'yansu mata ke da digiri na biyu—sai na ga wannan ai wulakanci ne", inji Hajiya Hafsat.

Marubuciyar dai na da 'ya'ya mata da suka yi karatu a fannoni daban-daban—babbar cikinsu ita ce fitacciyar 'yar jaridar nan Kadariyya Ahmed, autarta kuma kwanan baya ta kammala karatun jami'a.

Don haka ne ta yanke shawara cewa, "bari mu kalubalance shi, mu ba ma wani mukamin kwamishin muke so ya ba mu ba, kujerar tasa gaba daya muke so. Saboda haka na ce ni zan yi takarar gwamna".

Bayanan hoto,

Kwanan baya 'yar autar Hafsat Abdulwaheed (ta farko daga dama) ta kammala karatun jami'a

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sai dai kuma ba ta samu yin takarar ba, duk da cewa ta buga fosta ta yi komai saboda, a cewarta, a kasar Hausa ba a saba jin mace za ta yi wani abin kirki ba balle shugabanci, don haka har azumin aka yi na kwana uku aka tsine mata.

Wannan ne ya sa jam'iyyar da take son yi wa takara ta hana ta, sannan daga bisani mahaifinta ya ce kada ta sake maganar yin takara. Da haka ta hakura.

Da dai marubuciyar ta yi wannan takara, to da ta cimma abu biyu—na farko da ta zama mace ta farko da ta yi takarar gwamna a Jihar ta Zamfara; na biyu kuma da ta kawar da wani tunani musamman a fagen siyasar Najeriya na cewa sai dan asalin wuri ne zai iya takarar neman mukami.

Ita dai Hafsat Abdulwaheed an haife ta ne a birnin Kano a shekarar 1952, kuma a nan ta yi karatunta na firamare da sakandare da difloma. Bayan ta yi aure ne ta koma Gusau, babban birnin Jihar Zamfara—lokacin jihar na karkashin Jihar Sakkwato—inda maigidanta ke rike da mukamin manaja a kamfanin John Holt.

Ta fara rubuce-rubuce ne lokacin tana aji uku a makarantar firamare, inda takan rubuta tatsuniyoyi, har ma ta samu kyaututtuka.

Lokacin tana aji uku ko hudu a makarantar firamare Hukumar Raya Al'adu ta Burtaniya, wato British Council, ta ba ta kyautar yabo saboda rubuce-rubucen da take yi.

Mai yiwuwa wannan kyauta ce ta bude mata kofofin wasu kyaututtukan da ta samu daga bisani don yabawa da gudummawar da take bayarwa a kan harkar adabin Hausa.

Bayanan hoto,

Hafsat Abdulwaheed ta karbi kyaututtuka da lambobin yabo da dama saboda gudunmawar da ta bayar ga harkar adabin Hausa

Kadan daga cikin kyaututtukan sun hada da wadda gwamnatin Jihar Kano ta taba ba ta, da wadanda kungiyoyin marubuta daban-daban suka ba ta, da ma wadanda aka ba ta yayin wadasnu manyan tarurruka a kan adabi.

Amma kafin nan, wani labari da Hafsat ta rubuta ta kuma shiga gasar rubuce-rubuce da shi a 1970 ya zo na biyu, shi ne koma littafinta na farko da aka wallafa kuma littafin kagaggen labari na Hausa na farko da aka wallafa wanda wata mace ta rubuta.

"Ina aji biyar na makarantar firamare na rubuta So Aljannar Duniya, saboda a lokacin ne yayata ta yi aure. To kuma da yake wanda ta aura din ba yarenmu day aba, ta samu 'yar matsala; [wannan matsala ce] ta sa na rubuta littafin".

Amma daga bisani ta yi wa littafin kwaskwarima kafin ta shigar da shi gasa, inda ya tabo batun auren dole.

Hajiya Hafsat Abdulwaheed ta rubuta littattafai fiye da talatin, amma kusan guda biyar ne kawai aka wallafa suka shiga kasuwa.

Littattafan da aka wallafan sun hada da So Aljannar Duniya, da 'Yar Dubu Mai Tambotsai (wadannan biyun littattafan tatsuniya ne), da Nasiha ga Ma'aurata (wanda ke magana a kan yadda za a kyautata rayuwar aure), da Namijin Maza Tauraron Annabawa (tarihin Annabi Muhammadu, tsira da aminci su tabbata a gare shi) da kuma na baya-bayan nan, Ancient Dance (littafin wake na Ingilishi).

Akwai kuma littafin Saba Dan Sababi, wanda littafin gajerun labarai ne da take fatan rubuta mujalladi hudu, amma zuwa yanzu ta kammala na farko.

Kusan 18 daga cikin rubuce-rubucen Hafsat Abdulwaheed dai na addini ne; a halin yanzu ma tana rubuta wani a kan mu'ujizozin Alkur'ani, saboda "na lura cewa a yanzu babu littattafan da ke magana a kan hakan sosai", inji ta.

Galibin rubuce-rubucen Hajiya Hafsat bas u kai ga wallafa ba saboda "rashin kudi".

A cewarta, "A da idan ka yi rubutu ka kai kamfani, kamar su Longman ko NNPC, za su karba su buga maka littafin, su dan ba ka royalty (kason da ake bai wa marubuta daga cikin kudin da ake samu idan an sayar da littattafansu), amma yanzu ba mu da wannan gatan".

To me zai hana ta rika wallafawa da kanta kamar yadda wadansu marubutan ke yi?

Bayanan hoto,

Hafsat Abdulwaheed na karanta daya daga cikin littattafanta

"Akwai bambanci tsakanin rubutuna da [irin] wadannan—abin da ya sa ba na haka shi ne ina so ya fito da inganci".

Sai dai kuma tana ganin a cikin marubutan da kan yi bugun kasuwa akwai wadanda rubutunsu ke da inganci, duk da cewa littattafan ba su da inganci.

Yawan sakin mata na cikin dalilan da ke ci wa Hajiya Hafsat tuwo a kwarya, kuma ta yi rubuce-rubuce a kan haka. A ganinta, akwai bukatar ma'aurata su rika hakuri da juna ko don kauce wa jefa 'ya'yan da suka Haifa cikin mugun hali sakamkon mutuwar auren.

Daga cikin litttattafan da suka taimaka wajen kaifafa basirar marubuciyar a kan harkar rubutu akwai Magana Jari Ce da Ruwan Bagaja na Abubakar Imam.

Sai dai kuma ta ce ita a ganinta Imam ba marubuci ba ne, manazarci ne: "…Bai taba rubuta wani abu shi kadai ba, sai tafiyarshi Ingila. Shi an bas hi littattafai ne ya yi nazari a kai ya fitar da labarai—an ba shi Alfu Laila, an ba shi Ikra, littattafan tatsuniyoyi na Larabawa.

"In aka ban littafi yanzu, aka ce in fitar da littattafai, wallahi ko dubu ake so zan iya fitarwa in dai za a ba ni labaran—kamar yanzu a dauko tatsuniyoyin Ingila ko na Scotland a ba ni a ce na fitar da littattafan Hausa ba zai min wahala na ftar da sub a".