'Nigeria ce ta biyu a cuta mai karya garkuwar jiki'

Najeriya ce ta biyu bayan Afirka ta Kudu
Bayanan hoto,

Akwai mutane miliyan 37 masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki a duniya

Wani tsohon jami'in Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da hada yaduwar cutar Ƙanjamau ko kuma HIV/AIDS, a Uganda, Musa Ahmed Bungudu, ya ce Najeriya ce ta biyu a cutar a fadin duniya.

Tsohon jami'in ya ce kasar Afirka ta Kudu ce ta farko a yawan mutanen da ke dauke da kwayar cutar ta ƘAnjamau.

Alhaji Bungudu ya kara da cewa a Najeriyar an haifi jarirai kimanin dubu 60 masu dauke da kwayar cutar.

Ya kuma ce rashin mayar da hankali wajen dakile cutar ne ya janyo wa Najeriyar halin da take ciki.

Dangane kuma da nasarorin kan yakar cutar, Bungudu ya ce, wasu kasashen na Afirka sun yi samu nasara amma fa banda Najeriya.

Akwai dai kimanin mutane miliyan 37 da ke dauke da wannan cuta a fadin duniya.

Ranar 1 ga watan Disambar kowace shekara, ta kasance ranar yaki da cutar mai karya garkuwar jiki, ta duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta ware ranar da manufar wayar da kan al'umma a kan illolin da ke tattare da cutar, da kuma hanyoyin da za abi wajen hana yaduwarta da ma rashin kamuwa da ita.