Colombia na bincike kan ko rashin mai ne ya yi sanadin hatsarin jirgi

Magoya bayan 'yan wasan sun taru a filin wasan Atletico Nacional stadium da ke Medellin domin nuna alhini

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Magoya bayan 'yan wasan sun taru a filin wasan Atletico Nacional stadium da ke Medellin domin nuna alhini

Hukumomi a kasar Colombia sun ce shaidun da suka tattaro sun nuna cewa man da ya kare a jirgin ne ya yi sanadin faduwarsa.

Jirgin, wanda ya yi hatsari ranar Litinin a kusa da Medellin, na dauke da mutum 77 akasarin su 'yan wasan wata kungiyar kwallon kafar Brazil, kuma mutum shida ne kawai suka tsira.

Wani bincike da masana jirgin sama suka gudanar a wurin da jirgin ya fadi ya nuna cewa "babu mai a cikin jirgin" lokacin da ya fadi.

Wannan binciken ya yi daidai da wasu bayanan sirri da aka kwarmata wa 'yan jarida, wadanda suka samo daga na'urar nadar magana a cikin jirgin.

A cikin na'urar dai, an ji direban jirgin yana neman izinin yin saukar gaggawa saboda lalacewar na'ura da kuma rashin mai a cikin jirgin.

Shugaban fannin kula da jiragen sama Alfredo Bocanegra ya shaida wa wani taron manema labarai cewa, "Muna so mu tabbatar cewa binciken da muka yi ya nuna cewa jirgin ba shi da mai a cikinsa lokacin da ya fadi."

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Yawancin masu goyon bayan 'yan wasan Chapecoense sun barke da kuka a filin wasan Chapeco na Brazil