Shugaban Gambia na fuskantar gagarumin kalubale a zabe

Shugaba Jammeh na Gambia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yahya Jammeh ya kwashe shekara 22 a kan mulki

'Yan kasar Gambia na kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da ake sa ran yin kankankan tsakanin fitaccen mai harkar gidajen nan Adama Barrow da Yahya Jammeh, wanda ya kwashe shekara 22 a kan mulki.

Gwamnatin kasar ta katse intanet da wayoyin da ke kiran kasar daga kasashen waje a ranar zaben.

Akasarin jam'iyyun hamayya sun dunkule wuri guda inda suke goyon bayan Mr Barrow domin ya kayar da Mr Jammeh, wanda ya ce Allah zai ba shi nasara ya lashe zaben a karo na biyar.

Mr Jammeh ya musanta zargin cewa yana murkushe 'yan hamayya.

Kasar Gambia ba ta taba gwada mulkin dimokradiyya ba tun da ta samu 'yanci daga Birtaniya a shekarar 1965.

Masu sanya ido sun ce Mr Barrow, wanda rahotanni ke cewa ya taba zama jam'in tsaro a kantin sayar da kaya na Argos da ke Birtaniya, ya samu gagarumin goyon baya daga wajen 'yan hamayya.

Masu kare hakkin dan adam sun zargi Mr Jammeh, wanda a baya ya yi ikirarin cewa zai warkar da masu cutar kanjamau da ta rashin haihuwa, da cin zarafin 'yan adawa.

An daure fitattun 'yan adawa da dama a gidan yari tun bayan da suka yi wata zanga-zanga a watan Afrilu.

Masu sanya ido a kan zabe daga kungiyar tarayyar Turai da Ecowas ba za su halarci wajen zaben ba.

Sai dai kungiyar tarayyar Afirka ta aike da masu sanya ido a kan zaben.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Adama Barrow na fatan kayar da Jammeh