Trump ya nada 'mahaukacin kare' a muƙamin sakataren tsaro

Janar James Mattis ya yi kaurin suna wajen caccakar Obama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Janar James Mattis ya yi kaurin suna wajen caccakar Obama

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya nada James Mattis, tsohon fitaccen sojan ruwan nan da ya yi yaki a Iraqi da Afghanistan, a matsayin sakataren tsaron kasar.

Trump ya ce, Janar Mattis mutum ne "ƙwararre", a lokacin da yake yin jawabin ba shi mukamin a jihar Ohio.

Janar Mattis, wanda ake yi wa lakabi da "mahaukacin kare", mutum ne da ya saba yin katobara, wanda kuma ya fi suna wajen caccakar shirye-shiryen gwamnatin Obama kan yankin Gabas Ta Tsakiya, musamman kasar Iran.

Ya taba bayyana Iran a matsayin "kasa daya tilo da ta fi yin barazana ga zaman lafiyar a Gabas Ta Tsakiya".

Mr Trump ya yi bayar da sanarwar nadin Janar Mattis ne a Cincinnati lokacin fara gangamin "Godiya ga Amurkawa na shekarar 2016".

Ya shaida wa magoya bayansa cewa, "Za mu nada 'Mahaukacin kare' a matsayin sakataren tsaronmu. An ce shi ne mafi kusanci ga Janar George Patton, fitaccen mutumin da ya yi yakin duniya na biyu."

A baya dai Mr Trump ya bayyana Janar Mattis, mai shekara 66, a a matsayin "Janar din da babu kamarsa".

Shi ne mutumin da ya jagoranci bataliyar Amurka a yakin tekun fasha na shekarar 1991 da kuma hadin gwiwar jami'an tsaro a kasar Afghanistana shekarar 2001.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mr Trump yana gangamin nuna godiya ga magoya bayansa

Yana cikin sojojin da suka mamaye Iraqi a shekarar 2003 sannan shekara daya bayan haka ya taka muhimmiyar rawa a yakin da aka yi a Fallujah.

Janar Mattis ya yi ritaya a shekarar 2013 bayan ya zama kwamandan rundunar sojin Amurka ta tsakiya.