Manyan birane hudu za su daina tuka motoci masu aiki da gas a 2025

Gurbatacciyar iska a Paris

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gurbatacciyar iskar da ke damun birnin Paris ta sa shugabannin daukar wannan mataki

Shugabannin manyan birane hudu na duniya sun ce za su daina amfani da motocin da ke aiki da gas nan da tsakiyar karni mai zuwa.

Shugabannin biranen Paris, Mexico City, Madrid da kuma Athens sun ce za su dauki matakin ne domin inganta iskar da mutane ke shaka.

Sun kara da cewa za su bayar da ladan kudi ga duk mutumin da ya daina amfani da mptocin da ke aiki da gas da kuma mutanen da suka koma takawa a kasa ko kuma hawan keke.

Shugabannin sun bayyana hakan ne a taron da suka yi a Mexico.

A 'yan shekarun baya bayan nan, ana ta sukar yin amfani da motoci masu aiki da gas saboda yadda suke gurbata muhalli.

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta ce kusan mutum miliyan uku ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon cutukan da ke da alaka da iska mai gurbata muhalli.

Ababen hawan da ke amfani da gas suna fitar da gurbatacciyar iskar nitrogen oxides, wacce ke yin illa ga huhu da hanyoyin numfashi, lamarin da kan yi sanadin mutuwar mutum.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Birnin Madrid zai hana amfani da ababen hawa masu aiki da gas kafin 2025