Mata 100: Likitoci mata uku 'yan gida daya

Bayanan sauti

Irin kalubalan da mata likitoci ke fuskanta

Farfesa Hadiza Shehu Galadanci ita ce babba kuma likitan farko a cikin yara takwas a gidansu.

Likitan mata ce kuma tana aiki a asibitin koyarwa na Aminu Kano, da ke birnin Kano a arewacin Najeriya.

Kannenta Aisha Amal da Jawhara duka suma likitoci.

Dakta Hadiza ta ce tun tana yarinya ta ke da sha'awar ta zama likita saboda ta taimakawa mutane.

Ta bayyana cewa ta kware ne a fannin kula da cututtukan mata saboda rashin kwararru a fannin kula da mata a wancan lokacin a asibitotcin da ke Kano.

Ta ce "harkar da ta shafi mata, ya kamata a ce akwai mata da dama da suka shiga wannan fannin".

Dakta Aisha Amal Galadanci ita ce likita ta biyu a gidansu kuma tana aiki ne asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano a bangaren jini.

Aisha ta ce ganin cewa yayarta ta zama likita, sai hakan ya ba ta sha'awada kwarin gwiwar yin karatun likita.

Likitan ta kara da cewa tausayin mutane ya kara jan hankalinta wajen sha'awar yin karatun likita wanda hakan ya sa ta yi karatun kwarewa a fannin jini.

Amma kuma dakta Aisha ta ce "aikin likita aiki ne wanda ke bukatar lokacin mutum baki daya".

'Rashin shiga cikin 'yan uwa'

A nata bangaren Dakta Jawhara Shehu Galadanci ita ce likita ta uku a gidansu kuma itama tana aiki ne asibitin Mallam Aminu Kano.

Kamar dai yadda yayunta biyu suka bayyana ita ma ta ce ganin cewa sun yi karatun likita, shi ne yasa ita ma ta yi sha'awar yin karatun domin bai wa al'umma gudunmuwarta a fannin lafiya.

Jawhara Galadanci ta shaida wa Yusuf Ibrahim Yakasai cewa ta fuskanci kalubale, musamman lokacin da ta ke karatun.

Ta ce "rashin shiga cikin 'yan uwa da rashin mu'amala da abokai na daya daga cikin irin kalubalen da na fuskanta".

Za ku iya sauraron cikakkiyar hira da sashin Hausa na BBC ya yi da wadannan likitoci a farkon wannan shafi.