An hana ECOWAS sanya ido a zaben Gambia

Marcel A. de Souza

Asalin hoton, ECOWAS

Bayanan hoto,

Masu sanya ido sun ce Mr Barrow ya samu gagarumin goyon baya daga wajen 'yan hamayya.

Bayanai sun nuna cewa hukumar zaben Gambia ba ta bai wa tawagar kungiyar raya kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS damar a zaben shugaban kasar da ake yi ranar Alhamis ba.

A wata sanarwa da hukumar kungiyar ta fitar ECOWAS din ta ce duk da haka ta na tare da al'ummar kasar Gambiya yayin da suke kada kuri'a kuma za ta tabbatar an bi ka'idoji zabe na kasa da kasa.

Sai dai bata bayyana yadda za ta tabbatar da hakan ba kasancewar babu jami'anta a cikin masu sa ido a zaben.

Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Marcel A. de Souza yana cewa kamar yadda yarjejeniyyar ECOWAS a kan dimokuradiyya da kyakyawan shugabanci ta tanadar, kungiyar na fatan ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Tuni dai aka bayar da rahoton cewa an tasho hanyoyin sadarwa a Gambiya, al'amarin da ya sa manazarta ke ganin za a tafka magudi a zaben.