Ana kisan kare-dangi a Sudan ta Kudu — UNCHR

Kisan kare-dangi da UNCHR ta ce ana kokarin yi a Sudan ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu da suke zauna a Juba

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai tabbatar da hakkokin bil-Adama, UNCHR, ta yi gargadin cewar ana kisan kare-dangi a kasar Sudan ta Kudu mai fama da yake-yake.

Ta kuma ce ta lura ana amfani da yunwa da kona kauyuka da ma fyade a matsayin wani salo na yaki a fadin kasar.

Hukumar mai mambobi uku, wadda aka kafa ta a bana, ba ta jima ba da kammala wata ziyara ta kwana 10 a kasar ta Sudan ta Kudu, wacce ta kwashe shekaru fiye uku cikin rikice-rikice.

Shugaba Salva Kiir ya musanta cewa ana yi wa wasu kabilu kisan kare-dangi.

A wata sanrwa da ta fitar ranar Alhamis, hukumar ta UNCHR ta ce, "Ana share fagen maimaita abin da ya faru a Rwanda" a 1994, tana mai ambatar kisan gillar da aka yi wa mutum 800,000, galibinsu 'yan kabilar Tutsi da 'yan kabilar Hutu masu sassaucin ra'ayi a cikin wata uku.

Shugabar mambobin ta hukumar, Yasmin Sooka, ta ce a duk wuraren da hukumar ta ziyarta a Sudan ta Kudu, ta ji "kauyawa suna cewa a shirye suke su ba da jininsu don kwato filayensu".

Yakin basasar Sudan ta Kudu ya tilasta wa mutum fiye da miliyan biyu tserewa daga gidajensu.

Hukumar ta ce ta fahimci ana kikrkirar yunwa da kona kauyuka da fade a matsayin garkuwa a lokutan da ake gwabza yaki a kasar.

Asalin hoton, Dr M Izady/www.gulf2000.columbia.edu

Bayanan hoto,

An fara rikicin ne a shekarar 2013, shekara biyu da Sudan ta Arewa ta samu 'yancin cin gashin kai.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A kwanan nan mambobi uku na hukumar da aka kafa a farkon shekarar nan suka kammala jiyarar aiki ta kwanaki goma a Sudan ta Kudu, wadda ke fama da rikici tsawon shekara uku.

Shugaba Salva Kiir ya musanta zargin ana kokarin kawar da jinsi.

A jawabin da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, UNCHR, ta ce "ana kokarin maimata abinda ya faru a Rwanda" a 1994 - inda aka kashe mutane 800,000 yawansu 'yan Tutsi da 'yan Hutu suka yi a cikin wata uku.

Babban jami'i na UNCHR, Yasmin Sooka ya ce duk inda tawagarsu ta shiga a Sudan ta Kudu suna jin mutane a kauyuka na cewa a shirye suke a zubar da jini domin su kwato yankinsu.

Yakin basasa a Kudancin Sudan ya yi sanadiyyar raba mutane sama da miliyan 2.2 da suka tserewa gidajensu.

An fara rikicin ne a shekarar 2013, shekara biyu da Sudan ta Arewa ta samu 'yancin cin gashin kai, bayan da Shugaba Salva Kiir ya kori makarrabansa da kuma zargin mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa da ba a yi nasara ba.