An fara zaben sharar-fage a Ghana don ma'aikata na musamman

Masu ayyuka na musamman na kada kuri'unsu a Ghana
Bayanan hoto,

Masu ayyuka na musamman na kada kuri'unsu a Ghana

A Ghana an fara gudanar da zaben shugaban kasa, inda aka ba wa masu ayyuka na musamman damar kada kuri`unsu gabannin ranar babban zaben, wato Laraba mai zuwa, 7 ga watan Disamba.

Wadannan masu ayyukan na musamman din dai galibinsu jami`an tsaro ne da dangoginsu da kuma ma`aikatan hukumar zabe da malaman da aka dauka don taya ta aikin zaben.

Sai dai ana fuskantar matsala, kasancewar wasu masu zaben basu ga sunayensu ba a rijistar mazabunsu.

Tun da farko jam`iyyun adawa sun koka dangane da jinkirin da hukumar zaben kasar ta yi kafin ta baje-kolin sunayen masu zaben, Lamarin da suka yi zargin cewa dabara ce ta ba wa jam`iyya mai mulki kafar yin magudi, amma hukumar zaben ta musanta.

Masu ayyuka na musamman da dama dai na ta yin wadari daga wannan mazaba zuwa waccan da fatan za su ga sunayensu.

Hukumar zabe a nata bangaren ta ce tana bakin kokarinta don magance matsalar.

Kimanin masu ayyukan na musamman dubu 140 ne suke kada kuri'unsu.