Nigeria: '$19m za su kai-komo tsakanin mutane saboda N-Power'

A dauki matasa dubu 200 a kashin farko na shirin N-Power
Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya yi alkawarin rage matsalar rashin aikin yi

Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce sakamakon shirin daukar matasa dubu 200 aiki da gwamnatin kasar ta yi, za a samu kusan $19m da za su kai-koma a hannun 'yan kasar.

Wasu dai na ganin cewa shirin na N-Power da gwamnatin Najeriya ta fara aiwatarwa ranar Alhamis, kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.

Suna kuma bujuro da dalilin yawan matasan kasar da ba su da aikinyi da sun kai miliyoyi.

Sai dai kuma Abubakar Aliyu wanda masanin tattalin arziki ne a Najeriya, ya ce Naira dubu 30 din da za a rinka biyan matasan su dubu 200, a kowane wata, yawanta zai kama Naira Biliyan shida wato kwatankwacin Dala miliyan 19.

Ya kuma kara da cewa kudin za su kai-komo ne a tsakanin 'yan kasar, al'amarin da zai bunkasa yalwar arziki sannan kuma ya farfado da tattalin arzikin al'umma.

Ku saurari yadda hirarsa masanin ta kasance da Muhammad Kabir Muhamma:

Bayanan sauti

Hira kan amfanin shirin N-Power