Ghana 2016: Rawar da kudi ke takawa a zabe

Addo ya sha zargin John Mahma da lalata tattalin arzikin Ghana
Bayanan hoto,

Dan takarar jam'iyyar NPP, Nana Addo-Kuffor yana kalubalantar John Mahma

Kananan jam'iyyu a kasar Ghana sun fara karaya wajen shiga a fafata da su a zaben shugaban kasar da ma na majalisar dokoki.

Hakan ba ya rasa nasaba da yadda siyasar facaka da kudi ta mamaye zaben kasar na 2016.

Jam'iyyar CPP ta marigayi Kwame Nkurumah, ta ce, ba za ta iya shiga takarar shugaban kasa ba saboda facakar da jam'iyyu masu karfi suke yi da kudade.

Domin haka, ta ce, za ta yi takarar neman kujerun majalisa ne kawai.

To amma manyan jam'iyyu irin su NDC da NPP sun ce kudaden da suke amfani da su a harkar kamfe suna samun su ne daga harajin da ake dorawa 'yan jam'iyya.

Ana dai ganin cewa yawancin 'yan takarar da ke facaka da kudi lokacin kamfe, sun samo kudin ne daga lalitar gwamnati.

Rahotanni dai sun ce jam'iyyu masu karfin tattalina arziki suna raba wa masu zabe tufafi da kayan ƙawa da ma kayan abinci masu dauke da hotunan 'yan takara.

A ranar Laraba mai zuwa ne dai za a kada kuri'ar zaben shugaban kasar ta Ghana da 'yan majalisu.

Fafatawar neman shugabancin kasar, ya fi zafi tsakanin manyan jam'iyyun kasar guda biyu wato NDC mai mulki da kuma NPP ta adawa.

Shugaba John Dramani Mahma wanda shi ne shugaban kasar mai ci, yana neman tazarce a karkashin jam'iyyar ta NDC.

A inda ita kuma jam'iyyar NPP, ta tsaiyar da Nana Akufo-Addo domin kalubalantar shugaban mai ci.