An wanke Didier Drogba daga zargin cin hanci

Drogba ya ce zai bar Montreal FC a watan Nuwamba

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Drogba ya ce zai bar Montreal FC a watan Nuwamba

Wani bincike da aka yi kan gidauniyar da tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba ke gudanarwa ya gano cewa bai yi zamba-cikin-aminci ko cin hanci ba sai dai watakila ya yaudari masu bayar da agaji.

An soma binciken ne kan "wasu bayanai masu tayar da hankali" a gidauniyar ta the Didier Drogba Foundation a watan Afrilu.

Hakan ya faru ne bayan wani rahoto da jaridar Daily Mail report ta wallafa da ya yi zargin cewa dan wasan ya kashe £14,115 cikin gudunmawar £1.7m da aka bai wa gidauniyar domin yin aiki a Afirka.

Drogba, mai shekara 38, ya bukaci jaridar ta ba shi diyya sannan ta nemi gafararsa kan kazafin da ta yi masa.

Sai dai hukumar da ta yi binciken ta gano cewa dan wasan bai aikata laifi ba.

Sai dai kawai ta ce bai kamata gidauniyar ta hada asusunta da na reshenta da ke Afirka ba.

Hakan na nufin ba a kashe kudaden da gidauniyar ta karba a Birtaniya domin inganta asibitoci, kamar yadda aka shaida wa masu bayar da tallafi cewa za a yi.

Rahoton ya kara da cewa, "Masu bayar da tallafi sun yi tsammanin za a yi amfani da kudaden da suka bayar wajen agazawa jama'a ba ajiye su a bankuna ba."